Maka Abubakar Malami a Kotu: Femi Falana ya yi Barazanar Haka
Lauyan da ke fafutikar kare hakkin bil adama, Femi Falana ya rubata wasika zuwa da Antoni Janar na gwamnatin Najeriya, Abubakar Malami ya na barazanar maka shi kotu idan ya ki daukan matakai kan kudaden da kotun koli ta bukaci a dawo da su $62bn daga wasu kamfanonin mai.
Falana ya aike wannan wasikar ga Malami a jiya Lahadi a madadin Farfesa Omotoye Olorode da Jaye Gaskiya na kungiyar People’s Alternative Political Movement.
Wani ɓangare na wasikar na cewa, “An bukaci mu yi maka tuni har yanzu gwamnati ba ta aiwatar da umarnin kotun koli ba na ranar 20 ga watan Oktoba”.
Falana ya jadada cewa duk da cewa an yanke hukunci a kan wannan matsayi, karaminin ministan man fetur, Timipre Sylva, na cewa ma’aikatar ba za ta iya dawo da wadannan kudade ba.