Makarantu Zasu Koma Karatu 18 ga Watan Janairu – Dakta Sani Aliyu

Makarantu zasu koma karatu ranar 18 ga watan janairu.

Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da korona ne ya bayyana haka.

Ya fadi hakan ne a wani shiri na gidan talabijin ranar Talata Fadar shugaban kasa a ranar Talata ta bayyana cewa za’a koma makarantu ranar 18 ga watan janairu a duk fadin Nigeria, saidai idan ma’aikar Ilimi ta saki wani abu makamancin haka, Kamar yadda The nation ta ruwaito.

Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da korona, Dr Sani Aliyu ne ya bayyana hakan a wani shirin gidan talabijin.

“A kan komawa makarantu, inaso na fayyace wani a abu, abundan ministan ilimi ya ce shine zasu waiwayi abun, bai ce za’a chanza ranar komawa ba, yace zasu waiwayi yanayin ne sannan su sanar da al’umma”. A cewar Aliyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here