Gwamna Seyi Makinde ya Lashe Zaben Fidda Gwani a Karo na Biyu
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya sake samun damar yin takarar gwamna a karo na biyu a karkashin jam’iyyar PDP.
Gwamnan ya sanar da lashe zabensa na fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a fadin kasar nan kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Ya zuwa yanzu dai, jihohi na ci gaba da sanar da sakamakon zabukan fidda gwani da ke gudana a fadin jihohin kasar nan.
Oyo- Gwamna Seyi Makinde, a ranar Alhamis, ya zama wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Oyo na jam’iyyar PDP.
Read Also:
A zaben fidda gwani da aka gudanar a filin wasa na Lekan Salami da ke Adamasingba, Ibadan, Makinde ya samu kuri’u 1,040 inda ya doke abokin takararsa Hazeem Gbolarunmi wanda ya samu kuri’u biyu, Tribune Online ta rawaito.
Kamar yadda jami’in zaben ya bayyana, Ben Obi wanda Abdullahi MaiBasia ya wakilta, Makinde ya zama dan takarar gwamnan jihar Oyo a jam’iyyar PDP bayan ya samu mafi yawan kuri’u.
Jimillar kuri’u shida ne marasa kyau daga cikin kuri’u 1,048 da aka kada.
Makinde ya yabawa ‘yan jiharsa da suka amince ya ci gaba da aiki daga inda ya tsaya bayan amince dashi a karo na farko bayan 2019, inji rahoton Punch.
Ya zuwa yanzu, jihohin Najeriya na ci gaba da kawo sakamakon zaben fidda gwani da ake ci gaba da gudanarwa, yayin da ake samun matsaloli na rarrabuwar kai a wasu jihohin.