Makwabtan Mali Sun Amince da Cire Takunkuman da Suka Sakawa Kasar
Kasashe makwabtan Mali za su dage takunkuman tattalin arzikin da suka sanya wa kasar, bayan kungiyar ECOWAS ta amince da shirin kasar na gudanar da zaben da zai mayar da mulki hannun farar-hula a watan Maris din shekarar 2024.
Haka kuma, ba a amince ko da daya daga cikin sojojin da suka yi juyin mulki, tsayawa takarar shugaban kasa, ba.
Read Also:
Sai dai har yanzu ECOWAS ba ta amince da komawar Mali cikin kawancen ba tun bayan dakatar da ita jim kadan bayan juyin mulkin sojin kasar.
Shugabannin kasashen Afirka ta yamma, sun amince da wa’adin shekara biyu domin gudanar da zabe a Burkina Faso yayin da a Guinea kuma aka yi watsi da wa’adin shekara uku na mika mulki ga farar hula.
Kasashen na Burkina Faso da Guinea suma kamar Mali sojoji ne suka hambarar da gwamnatocinsu na farar-hula.