Malamai a Jamhuriyar Nijar Sun Shiga Yajin Aiki
Ƙungiyar malaman kananan makarantu ta “(SYNACEB) reshen Makalondi ta jihar Tillabery a Jamhuriyar Nijar ta tsunduma cikin wani yajin aiki.
Malaman sun shiga yajin aikin na kwanaki biyu ne daga ranar Litinin domin janyo hankalin gwamnati ta ɗauki matakai na kare malaman daga matsalar tsaro.
Read Also:
Ƙungiyar ta ce ɗauki matakin ne bayan la’akari da abin da ya faru a ranar 27 ga watan Oktoban bara, inda ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu malaman makarantu biyu da kuma lamarin ranar 10 ga watan Janairu inda aka kashe wani malami bayan shafe tsawon lokaci a hannun ƴan bindigar.
Lamarin tsaro dai na ƙara taɓarɓarewa a jihar Tillabery duk da iƙirarin da shugaban majalisar mulkin sojin ƙasar yayi na cewa suna samun nasara a yaƙin.