Rashin Tsaro: Jerin Manyan ‘Yan Najeriya 4 da ‘Yan Bindiga Suka Kashe Cikin Sa’o’i 48

 

Yayin da rashin tsaro ya yi kamari a cikin kasar, wasu fitattun ‘yan Najeriya sun rasa rayukansu sakamakon harbe su da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi.

Legit.ng ta kawo maku jerin manyan yan Najeriya, wasu yan kasuwa da kuma yan siyasan da ‘yan bindiga suka kashe a cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

1. Ahmed Gulak

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige Ahmed Gulak, tsohon mai bada shawara na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Owerri, jahar Imo, Daily Trust ta ruwaito.

Gulak, jigo a jam’iyyar All Progresive Congress, APC, ya baro Owerri ne yana hanyarsa na komawa Abuja a ranar Lahadi lokacin da yan bindigan suka kashe shi.

2. Justice Stanley Nnaji

A daren ranar Lahadi ne wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba suka kashe tsohon alƙalin babbar kotun jahar Enugu, Justice Stanley Nnaji, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Nnaji, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Isi-Uzo, an harbe shi ne a kusa da wata cibiyar binciken cututtuka, lokacin da maharan suka tare shi suka fito dashi daga cikin motarsa.

Da yake tabbatar da kisan, kwamishinan yan sandan jahar Enugu, Mohammed Ndatsu Aliyu, yace ya ƙaddamar da bincike kan maharan da ba’a san ko su waye ba, waɗanda suka yi awon gaba da motar mamacin.

3. Linus Owuamanam

A ranar Asabar da daddare ne wasu yan bindiga da ba’a gano ko su waye ba sun harbe wani ɗan kasuwa, Linus Owuamanam, har lahira a Ibadan, babban birnin jahar Oyo, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗan kasuwan mai suna, Linus Owuamanam, yana cikin tuƙa motar bas yayin da lamarin ya faru dashi a kan hanyar Mokola-Sango Ibadan, jahar Oyo.

4. Okiemute Mrere

Hakazalika a ranar Asabar ne yan bindiga suka halaka shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, reshen jahar Imo, Okiemute Mrere.

An kashe Mrere a kan babban titin Owerri zuwa Fatakwal dake Owerri, The Punch ta gano hakan a ranar Litinin.

Babban jami’in hukumar ya tabbatar da hakan inda yace an ga gawar shugaban a daji da safiyar Lahadi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here