Nasarorin da Gwamnatin Shugaban ƙasa Buhari ta Cimma Zai Amfanar da Mutanen Zamani da Dama Masu Zuwa – Lai Mohammed

Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, yace ayyukan cigaban da gwamnati Buhari Tayi zasu amfanar da mutane da dama nan gaba.

Ministan yace ba a taɓa samun wata gwamnati ba da ta samu nasarori da kaɗan ɗin da take samu kamar wannan gwamnatin.

Ministan ya faɗi haka ne a Abuja, yayin da yake jawabi ga manema labarai a wurin bikin cikar gwamnatin shekara 2 a zango na biyu.

Ministan yaɗa labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammed, yace nasarorin da gwamnatin shugaban ƙasa Buhari ta cimma zai amfanar da mutanen zamani da dama masu zuwa, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

Ministan ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, ba’a taɓa yin wata gwamnati ba a tarihin Najeriya data samu nasarori masu ɗimbin yawa da ƙarancin kuɗin shiga kamar gwamnatin shugaba Buhari.

Ministan Yace:

“Ba’a taba samun wata gwamnati ba a tarihin Najeriya da tayi ayyuka masu ɗimbin yawa da ƙaɗan ba kamar wannan gwamnatin.”

“Abu ne mai sauki a manta, amma lokacin da gwamnatin nan ta shiga ofis a 2015, farashin ɗanyen man fetur da ƙasar ta dogara da shi kashi 95% ya faɗi warwas a kasuwar duniya.”

“Hanyoyin mota da na jirgin ƙasa, gadar sama, samar da gidaje masu ɗimbin yawa, cigaban tashoshin ruwa, ƙarin samun hasken wutar lantarki da sauran ayyukan cigaba da Buhari yayi zasu amfana har ga mutanen da zasu zo nan gaba.

naija breaking news today

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com