Ina Maraba da Gwamna Matawalle ya Shigo APC – Jigo a Jam’iyyar APC a Zamfara
Martani na ci gaba da bin diddigin rahotannin da ke cewa Gwamna Bello Matawalle na iya ficewa daga PDP zuwa APC.
Wani jigo a jam’iyyar APC a Zamfara, Aminu Sani-Jaji, ya tashi tsaye kan batun na komawar gwamnan APC.
Dan siyasan bai yarda da mambobin jam’iyyarsa ba wadanda ke adawa da sauya shekar gwamnan Zamfara Wani jigo a jam’iyyar APC a Zamfara, Aminu Sani-Jaji, ya ce yana maraba da Gwamna Bello Matawalle ya shigo jam’iyyarsu ta APC.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa Sani-Jaji ya yi wannan bayanin ne a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Litinin, 19 ga Afrilu.
Read Also:
Ya bayyana cewa gwamnan na Zamfara yana da dama ta kundin tsarin mulki ya shiga kowace jam’iyyar siyasa da yake so.
Dan siyasar ya ce:
“A gare ni rashin sauya shekar Matawalle zuwa APC ya saba wa hakkinsa na tsarin mulki kamar yadda sashi na 40 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da aka gyara ya tanada.
“Idan kundin tsarin mulki ya ba da damar walwala a kungiyar siyasa to wanene zai hana Matawalle ko wani mutum sauya sheka zuwa APC? Ina tsammanin wadanda ke haifar da irin wannan tunanin ba masana ba ne na dimokiradiyya.”
Jigon na APC ya caccaki mambobin jam’iyyarsa da ke barazanar shigar da karar gwamnan idan ya sauya sheka daga PDP. Ya nisanta kansa da duk wani mai adawa da rahoton da Matawalle ya bayar na komawa APC.