Idriss Deby: Shugaba Buhari ya Mika Ta’aziyya ga Iyalai da Ilahirin Al’ummar Kasar Chadi

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harbe shugaban kasar Chadi da aka yi.

Ya kuma mika ta’aziyya ga iyalai da ilahirin al’ummar kasar Chadi bisa wannan babban rashi.

Karshe ya bayyana cewa rashin shugaban zai haifar da babban gurbi a kokarin yaki da Boko Haram.

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ce rasuwar shugaban kasar Chadi Idriss Deby “tabbas zai haifar da babban gurbi a kokarin da ake yi na hada karfi da karfe wajen tunkarar ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma Daular Musulunci ta Afirka ta Yamma.”

Shugaban ya yi wannan bayanin ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin sa Garba Shehu, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Deby ya mutu ne sakamakon raunin da ya samu yayin fada da ‘yan tawaye a arewacin kasar, a cewar sojojin Chadi a safiyar ranar Talata.

Wannan sanarwar mai ban tsoro ta zo ne kwana daya kacal bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya ba shi damar wa’adin mulki na shida.

Da yake maida martani kan lamarin ranar Talata, Shugaba Buhari ya ce “ya yi matukar kaduwa da dimautuwa game da mutuwar kwatsam ta Idriss Deby a fagen daga don kare ‘yancin kasarsa.”

A cewar shugaban, “Marigayi Deby ya taka rawar gani a hadin gwiwar yankin da muke da shi a yakin soja kan ‘yan ta’addan Boko Haram.”

Ya kara da cewa “mutuwar Deby tabbas za ta haifar da babban gurbi a kokarin hada karfi da karfe don tunkarar ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma Daular Musulunci ta Afirka ta Yamma.”

Yayin da yake jajantawa mutanen Chadi da sabon shugabansu, Shugaba Buhari ya yi kira da a kara hadin gwiwa domin fatattakar ‘yan ta’addan.

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here