Zaben Gwamnoni: Jam’iyyar LP ta Marawa PDP Baya a Jihar Rivers
Jam’iyyar Labour reshen jihar Rivers da kungiyar gangami ta Obi-dient Movement sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar gwamnan PDP a jihar, Sim Fubara a zaben 11 ga watan Maris.
Read Also:
Shugaban jam’iyyar Labour na jihar, Dienye Pepple ne ya bayyana hakan, inda ya ce shawarin ya zo ne duba da samar da daidaito da adalci a jihar, The Nation ta ruwaito.
Pepple, wanda ya jagoranci sauran shugabannin jam’iyyar don marawa Fubara a Fatakwal ya bayyana cewa, mazabarar Fubara ta Kudu maso Gabas har yanzu bata samar da gwamna ba a Rivers.
Ya ce, dukkan ‘yan jam’iyyar Labour sun yanke shawarin kada kuri’unsu ga dan takarar gwamnan a zaben mai zuwa don ci gaban jihar.
Karin bayani na nan tafe…