Fadar Shugaban Kasa ta yi Martani Kan Maganganun Bishop Kukah

 

Bai kamata a zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da haddasa rabuwar kai a Najeriya ba a cewar Femi Adesina.

A sakamakon haka ne Femi; mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya zargi masu sukar shugaban da raba kan ‘yan kasa

A cewarsa, wadanda suka raba kasar da bakunansu, da munanan maganganu sakaka, su ne suka haddasa rabuwar kai.

Aso Rock Villa, Abuja – Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya wanke mai gidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari daga sukar da ake masa na cewa salon mulkinsa ya raba kan ‘yan Najeriya.

Wani Babban Limamin Katolika na Diocese da ke Sokoto, Matthew Kukah, a ranar Lahadi, ya yi kakkausar suka ga Buhari kan rashin tsaro, cin hanci da rashawa, da rarrabuwar kawuna a Najeriya.

Kukah ya bayyana kokensa a cikin sakonsa na Ista mai taken, ‘To mend a broken nation: The Easter metaphor’.

A cewar Bishop din, ‘yan siyasa sun lalata kowane fanni na rayuwa a Najeriya yayin da suke cin hanci da rashawa.

Sai dai a martanin da ya mayar kan batun Kukah, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce abin mamaki ne a ce wadanda suke da laifin haifar da rarrabuwar kawuna a Najeriya su ne ke zargin shugaban kasar da irin laifin da suka aikata.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter Adesina ya rubuta cewa:

“Wadanda suka raba Najeriya da bakunansu, da muggan maganganu, magana babu birki, su ne wai yanzu suke tuhumar Shugaba Buhari. Abin bakin ciki! Mugun nufinsu ba zai cika ba.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here