Masana’antu a Najeriya na Kokawa Kan Tsada da Kuma ƙarancin Man Dizal a Fadin ƙasar

 

Masu masana’antu suna ci gaba da kokawa game tsada da kuma ƙarancin man dizal a Najeriya.

Ƙungiyar dillalan man dizal a ƙasar ta yi gargadin cewa matuƙar hukumomi ba su ɗauki matakin da ya dace ba, to farashin makamashin zai kai wani matsayi da ba a taɓa gani ba a Najeriya.

Ƙungiyar masu gidajen burodi a Abuja ta ce akwai yiwuwar farashin burodin zai ninka kuɗinsa nan gaba kaɗan, bayan sun sayi litar dizal a kan naira 1,500 a ranar Laraba.

Mataimakin shugaban kungiyar masu masana’antu ta Najeriya Alhaji Ali Safiyanu Madugu ya ce ya kamata gwamnati ta shiga lamarin tun kafin abin ya kazance.

Shi kuwa Alhaji Ishaq Abdulraheem shugaban masu gidajen biredi na birnin Abuja cewa yake sun shiga halin ni ‘ya su, saboda, baya ga tsadar man dizal din akwai kuma tsadar kayan sarrafa burodin.

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN dai, tace wannan matsalar tana da nasaba da abubuwa da dama ciki har da tsadar dala da yakin Ukraine da Rasha sai kuma zargin da suke yi cewa hukumar kula da sufurin man fetur ta Najeriya.

Akwai kuma batun kin biyansu kudaden dakon man da suke yi zuwa sassan kasar yadda ya kamata.

Alhaji Farouk Ahmad shi ne shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin albarkatun man fetur din, wato Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority, kuma ko BBC ta tuntube shi game da zarge-zargen da ake yi musu bai amsa ba.

Amma bayanai na cewa shugaba Muhammadu Buhari a baya-bayan nan, ya yiwa Kungiyar IPMAN karin naira goma kan kudin tallafin dakon man da ake basu, wanda ake ganin zai sassauta lamura.

Sai dai a cewar Alhaji Bashir Dan Malam shugaban IPMAN shiyyar arewa, har yanzu ba su gani a kasa ba.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here