Mata Masu Buga Kwallon Kafa Sun Cancanci a Rika Biyansu Kudi Daidai da Maza ‘Yan Kwallo – Cyril Ramaphosa

 

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya ce mata masu buga kwallon kafa na kasar sun cancanci a rika biyansu kudi daidai da maza ‘yan kwallo.

Shugaban ya bayyana haka ne a bikin dawowar ‘yan wasan gida bayan sun ci gasar cin kofin kwallan kafa na matan Afirka, inda a wasan karshe suka ci Maroko 2-1 a karshen mako.

Mista Ramaphosa ya gaya wa matan wadanda ke masa sahewa cewa ,” An gaya min cewa ana biyan maza ninki goma kan abin da ake biyanku idan kun yi wasa.”

Tawagar ta mata ta Afirka ta Kudu Banyana Banyana ta yi nasarar doke mai masaukin baki ne ta dauki kofin bayan sau hudu tana zuwa wasan karshe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here