Jam’iyyar APC ta Sanar da Sanata Abdullahi Gobir a Matsayin Sabon Shugaban Majalisar Dattijai

 

Abuja – Jam’iyyar All Progressive Congress watau APC ta ayyana sunan ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sokoto ta gabas, Sanata Abdullahi Gobir, a matsayin jagoran majalisar Dattijai.

Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya aike wa majalisar Datttawa kuma shugaban majalisa, Sanata Ahmad Lawan ya karanta da zaman yau Laraba.

Sanata Gobir zai maye gurbin Sanata Yahaya Abdullahi (Mai wakiltar Kebbi ta arewa) biyo bayan murabus ɗin da ya yi daga mukamin jagoran majalisa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sanatan ya yi murabus daga muƙamin ne bayan ya ɗauki matakin sauya sheka daga APC mai mulki zuwa babbar jam’iyyar hamayya watau PDP.

Ku saurari ƙarin bayani…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here