‘Yan sanda Sun Kama Mata 2 Masu Kai wa ‘Yan Bindiga Makamai da Maza 32 Masu Satar Mota
Yan sanda sun damke mata masu kaiwa yan bindiga makamai.
Yan matan biyu sun bayyana yan bindigan da suke kaiwa makamai.
Kakakin hukumar yan sanda ya bayyana wasu barayin mota kuma.
Abuja – Jami’an hukumar yan sandan Najeriya sun damke wasu yan mata biyu masu kaiwa tsagerun yan bindigan da suka addabi mutan Arewacin Najeriya makamai.
Kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba, ya ce matan masu suna Aisha Ibrahim da Hafsat Adamu sun kasance masu kaiwa yan bindigan makami duk lokacin da suke bukata, PRNigeria ta rawaito .
Read Also:
Daya daga cikinsu
Aisha tace:
“Wasu lokuta akan bamu makamai daga Lafia ko Kaduna kuma ina samun nasaran kaiwa wani Babangida, wani dan bindiga.”
Ita kuwa Hafsat, ta bayyana cewa tana kaiwa yan bindiga makamai Kaduna daga Kujama, bisa umurnin wani Suleiman.
Hukumar ta bayyana shahrarrun barayin mota
Har ila yau, yan sandan sun damke wasu barayin da suka kware wajen satan mota a Kaduna, Kano da Jigawa, inda suke kaiwa kasashen Nijar, Kamaru da Chadi.
Kakakin hukumar yan sanda, CP Frank Mba yace an kwato na’urorin bude mota biyu, wanda ke taimaka musu wajen bude motocin da kuma lalata fasahar bibiyar mota.
Wadannan barayi sun hada da maza 32, da mata 2.