Gidauniyar Farfesa Gwarzo: Mata 131 a Garin Gwarzo Sun Amfana da Tallafin Dubu 30
Kimanin Mata 131 a Garin Gwarzo unguwar sabon layin Kara , a jahar Kano suka amfana da tallafin naira dubu 30.
Wanda Gidauniyar farfesa Abubakar Adamu Gwarzo ta raba musu domin samun jari wajen gudunar da sana’oi su na yau da Kullum.
Dakta Musa Abdullahi Sufi,Wanda ya jagoranci
Raba kudin ga mata ya bayyana cewa dallin fito da tsarin bada tallafi zai sa Mata su zama masu dogaro da kai,haka zalika zai inganta rayuwarsu wajen rage wasu matsalolin dake addabar su na yau da kullum ,inda ya shawarce su wajen mayar da Hankali Kan amfani da kudin da suka samu daga Gidauniyar Abubakar Adamu Gwarzo kan gina sana’ar su a cikin yankin.
Musa Abdullah Sufi na Mika tallafi ga Daya daga cikin Mata 30
Read Also:
Shima anasa bangaren daya daga cikin hadiman Gidauniyar, maji dadin Hausawan turai Alhaji Gambo Dan Zango ya yaba irin ayyukan da Gidauniyar ke yi a cikin birni da kauye,inda ya bayyana cewa akwai sauran ayyuka da farfesa Abubakar Adamu Gwarzo zai kara yi wa unguwar layin sabo Kara wajen inganta rayuwar su ta fanni kayyakin more rayuwa da suka shafi bada tallafin karatun,magani a asibiti,gyara wutan lantarki da makamantansu.
Hakazalika,Alhaji Ibrahim Ahmad ya kara da cewa, wanna ba sabon abu bane a yankin idan aka duba irin ayyukan alkhairi da Gidauniyar Abubakar Adamu Gwarzo ke yi a cikin garin Gwarzo da Kuma jahar baki daya, matan da suka Sami tallafin zamu dinga bibiyar su wajen gani kudin da aka Basu sun amfana dashi ta inda ake bukata.
Malama Abu Madu mai shekaru 40 ta ce, tallafin dubu 30 da Gidauniyar ta Ba ta z ata yi amfani da shi wajen Kara jari akan Sana’ar ta na yin man kuli-kuli.
Sahura idi mai shekaru shekaru 45 ta ce tallafin yazo daidai lokacin da take neman dauki domin Kara jarin kosai.
Itama zahra’u kabiru mai shekaru 20 ta bayyana cewa,kudin zai taimaka mata wajen fara yin kasuwanci a cikin garin.
Cikin jerin sana’oi da Mata keyi a cikin garin sun hada da noman shikafa,gero dawa, kuli-kuli, kosai da Koko,kayan tebur,kayan Miya da sauran su.