Faɗuwar Darajar Naira: PDP ta caccaki APC

Jam’iyyar hamayya ta PDP a Najerya ta caccaki APC kan marawa kalaman gwaman Babban bankin kasar wato CBN baya, kan yada darajar naira ke ci gaba da faɗuwa.

A wata sanarwa da PDP ta fitar dauke da sa hannun sakatarenta na kasa Kola Ologbondiya, ta ce kalaman Godwin Emefiele na zagon-kasa ga tattalin arziki da sake jefa rayuwar ‘yan Najeriya cikin matsanancin yanayi.

PDP ta zargi cewa APC na amfani da gwamnan CBN wajen rarraba da wawushe dukiyar kasa.

Jam’iyyar ta yi kira ga APC da gwamnatin shugaba Buhari ta fito ta gyara aika-aikanta da suka jefa naira cikin mawuyancin yanayi da kuma tabbatar da adalci da ayyuka a bayyane.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here