‘Yan Najeriya 330,000 na Gudun Hijira a Kasashen da ke Makwabta da Najeriya – Sadiya Umar Farouq

 

Ministar Jin-ƙai da kare Afkuwar Bala’i ta gwamnatin Najeriya Hajiya Sadiya Farouq, ta ce ‘yan ƙasar 330,000 na kudun hijira yanzu haka a kasashe makwabta saboda kazancewar matsalolin tsaro.

Sadiya Farouq ta shaida haka ne a lokacin wata tattaunawa kan matsalolin hijirar da ke addabar Najeriya a Landan.

Ta ce cikin dubban mutanen da ke hijira akwai, mutum 16,634 a Chadi, da 118,409 a Kamaru, sannan a Nijar akwai mutum 186,957.

Sanna ministar ta ce ma’aikatarta ta kaddamar da wasu shirye-shirye da za su taimakawa mutanen da ke cikin matsalolin bukatar agaji.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here