Bethel Baptist: An Saki Karin ɗalibai 10, Bayan Biyan Kuɗin Fansa

An sake sakin karin ɗalibai da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jahar Kadunan arewacin Najeriya bayan biyan kuɗin fansa.

An saki dalibai 10 a jiya Lahadi, a cewar kungiyar kiristoci ta CAN, yanzu mutum 11 suka saura.

Shugaban kungiyar reshen Kaduna, Joseph Hayab ya ce yanzu haka suna kokarin ganin a saki sauran ɗaliban.

Wannan shi ne rukuni na huɗu na ɗaliban da ake saki bayan garkuwa da su. Adadin ɗalibai 110 aka saki ko suka kubuta kawo yanzu.

A ranar 5 ga watan Yuli aka yi garkuwa da ɗaliban sakandaren Bethel 121 a jahar Kaduna.

An cafke uku daga cikin ‘yan bindigar wanda ‘yan sanda suka gabatar da su a makon da ya gabata.

Satar ɗalibai domin nema kudin fansa abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya, inda masu garkuwar ke neman milyoyin kafin sakin su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here