Tsohon Mataimakin Shugaban APC ya yi Martani Kan Dakatar da shi da Akai

 

Hilliard Eta, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa yankin kudu maso kudu ya ce dakatar da shi da jam’iyyar tayi ba bisa ka’ida bane.

Eta ya yi wannan jawabin ne a matsayin martani kan dakatar da shi da NEC na jam’iyyar tayi yayin taron da ta gudanar ranar Talata 8 ga watan Disamba.

Tsohon mataimakin shugaban ya ce ya shigar da kara a kotu don haka jam’iyyar bata da ikon dakatar da shi ko kiran taron na NEC.

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC, na kasa (kudu maso kudu), Hilliard Eta, da yi watsi da dakatar da shi da Kwamitin Zartarwa, NEC, na Jam’iyyar tayi don ba kan doka aka yi ba.

Kazalika, Eta ya bayyana taron na NEC inda aka yanke shawarar dakatar da shi a matsayin haramtatta kamar yadda yake cikin rahoton da The Punch ta wallafa.

Ya yi wannan jawabin ne a matsayin martani kan dakatar da shi da NEC na APC tayi yayin taronta karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Talata.

Ya ce, “Na riga na shigar da kara a kotu. Ya kamata lauyoyi daga cikinsu sun fada musu cewa ba za s iya yanke wannan hukuncin ba tunda na shigar da kara kotu.

“Abinda suka yi bata lokaci ne kawai domin ba NEC na jam’iyya bane ma ta zauna a taron. “Sakataren riko na jam’iyyar ba shi da ikon kirar taron NEC. Duba da cewa ba a warware karar da na shigar kotu ba, ina son in ce ba zai yiwu kayi gini ba tare da fili ba, idan ma ba kotu ne ta bada wani hukunci ba, taron na NEC da aka yi a ranar 25 ga watan Yuni bai halasta ba kuma duk wani mataki da aka dauka ba zai yi tasiri ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here