Gwamna Masari ya Fitar da Sababbin Matakan Shawo Kan Matsalolin Tsaro a Jaharsa

 

Gwamnatin Katsina da ke arewacin Najeriya ta dakatar da hada-hadar kasuwanci da datse wasu manyan tituna saboda matsaloli na tsaro.

Wata sanarwa da gwamnan jahar Aminu Bello Masari ya fitar na cewa daga cikin matakan da ya dauka domin shawo kan matsalolin tsaron har da rufe wasu kasuwanni da kuma bin wasu tituna.

Sanarwar ta ce daga yau Talata 31 ga watan Agusta an rufe babban titin Jibia-Gurbin Baure, da umartar fasinjoji da matafiya su sauya hanya ta Funtua.

Sannan an rufe titin Kankara-Sheme ga duk ababen hawa na ƴan kasuwa, motocin gida kawai ne za su iya ratsa hanyar.

Gwamnan ya kuma haramtawa manyan motoci da ke shiga dazuka kwaso itatuwa.

An dakatar da cinikin dabbobi a kananan hukumomin Jibia da Batsari da Safana da Danmusa da Kankara da Malumfashi da Charanchi da Mai’auda da Kafur da Faskara da Sabuwa da Baure da Dutsinma da kuma Kaita.

Sannan an haramta cinikin dabobbi tsakanin Katsina da sauran jahohin Najeriya.

Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya hana daukan mutum 3 a babur ko keken A Dadaita Sahu, da haramta sayar da babur din hannu a kasuwar Charanchi.

Sannan an sanya dokar hana zirga-zirgar babura tsakanin 10 na dare zuwa 6 na safe a birnin Katsina, 6 na dare zuwa 6 na safe a baki daya kananan hukumomin jahar.

An hana sayar da man fetur a jarka, kuma ba a yarda gidajen mai a kananan hukumomi su sayar da man fetur da ya haura naira dubu biyar ba ga mutum.

Sai dai dokar hana zirga-zirga ba za ta shafi masu aiki na musamman ba irinsu, ma’aikatan lafiya da tsaro da ƴan jarida.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here