Matakin Sojoji Kan Masu Aikata Miyagun Laifuka ba Mafita Bane ko Hikima – Sheikh Gumi

 

Sheikh Ahmad Gumi ya sake jaddada ra’ayinsa na cewa ya kamata gwamnati ta zauna tattaunawa da ‘yan ta’adda.

A cewarsa, yadda sojoji ke ragargazar ‘yan bindiga ba zai zama mafita ga matsalar rashin tsaro a Najeriya ba.

Ya ce ya kamata gwamnati ta dauki matakan tattaunawa fiye da matakan yakar ‘yan ta’adda a yankin Arewa.

Kaduna – Babban malamin addinin Islama mazaunin jahar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi ikirarin cewa farmakin da sojoji ke kaiwa kan ‘yan bindiga da ke addabar Arewa maso Yamma ba zai magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta ba.

Malam Gumi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 6 ga watan Satumba ta shafinsa na Facebook, yayin da yake mayar da martani kan nasarorin da sojoji ke samu a kan ‘yan bindiga a dazuzzukan Zamfara.

Sanarwar, mai taken: ‘Zamfara: The Flaring of Crisis’, ta jaddada cewa matakin sojoji kan masu aikata miyagun laifuka “ba mafita bane ko hikima”.

A cikin sanarwar, Gumi ya bayyana yadda gwamnati ke tafka asara wajen kashe kudade don sayen makamai da jiragen yaki kuma babu wani sauyi a yakar ‘yan bindiga, wanda a cewarsa, zai durkusar da tattalin arzikin kasar.

Sanarwar ta ce:

“Abin takaici, wannan ba mafita bane ko hikima. Lokacin da ba ku da ikon kayayyakin aikin dakile tashin hankali, to tattaunawa tana da ikon warware rikici.

“Wannan shi ne abin da Majalisar Dinkin Duniya ke nufi. watau kudurin daidaita rikice-rikice. Abin da muke gani ya wuce masu ‘yan ta’adda da ta’addanci kawai, eh yana iya farawa kamar haka amma kamar kowane rikici, yana da sarkakiya.”

Mutane da dama sun fi bukatar tattaunawa fiye daukar matakan sojoji

A cikin sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo, Gumi ya kara bayyana cewa, ya tattauna da ‘yan bindiga da dama kan yadda za su mika wuya da kuma tattaunawa dasu.

Hakazalika, ya bayyana cewa, ya gana da gwamnoni da shugabanni da yawa, sun kuma tabbatar da zabin tattaunawa da ‘yan bindiga fiye da daukar matakan sojoji.

A cewar sanarwar:

“Na gana da yawancin shugabannin ‘yan bindiga don neman mafita daga wannan matsala. Na tattauna da ‘yan siyasa da jami’an tsaro.

Ban da ‘yan kalilan, yawancin gwamnonin jahohi suna son a warware rikicin cikin lumana. “Yan sanda da sauran jami’an tsaro suma sun fahimci girman matsalar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here