Ogun: Bata Gari sun Kashe DCO Sun yi Awon Gaba da Makamai Kuma-DPO ya Bata
Matasa masu zanga-zanga sun kashe DCO na ofishin ‘yan sandan da ke Atan-Ota, DSP Augustine Ogbeche
Matasan sun banka wa ofishin ‘yan sandan wuta inda suka raunata DPO wanda har yanzu ba a san inda yake ba – A cikin hakan, wani matashi farar hula ya rasa ransa yayin da suke kwashe makamai daga ofishin ‘yan sandan da suka saka wa wuta Fusatattun masu zanga-zanga a ranar Laraba sun kashe babban jami’in binciken laifuka, DSP Augustine Ogbeche tare da banka wa ofishin ‘yan sanda na Atan-Ota Ado-Odo da ke karamar hukumar Ota ta jihar Ogun wuta. Masu zanga-zangar sun raunata DPO na ofishin, SP Sikiru Olugbenga sannan har yanzu ba a san inda yake ba. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, The Punch ta wallafa.
Read Also:
Oyeyemi ya ce daya daga cikin farar hular masu zanga-zangar ya rasa rayuwarsa yayin da suke kone wani ofishin ‘yan sanda da ke Obada-Oko ta karamar hukumar Ewekoro. Ana amfani da ofishin a matsayin babban ofishin ‘yan sanda na musamman da ke yaki da fashi da makami
Oyeyemi ya ce, “Abun takaici ne yadda zanga-zangar lumana ta matasa a jihar Ogun ta koma rikici. Wasu bata-gari sun yi amfani da damar wurin aikata miyagun laifuka. “A safiyar Laraba, masu zanga-zangar sun kai hari ofishin ‘yan sanda da ke Atan-Ota inda suka banka masa wuta sannan suka kashe DCO, DSP Augustine Ogbeche. “Wani farar hula ya rasu sannan sun yi awon gaba da makamai. Sun raunata DPO, SP Sikiri Olugbenga wanda har yanzu ba a san inda yake ba. “Hakazalika a Abeukuta, wata kungiyar matasa ta kai hari ofishin ‘yan sanda na Obada-Oko inda suka tarwatsa ta.” Kakakin rundunar ‘yan sandan ya sanar da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Edward Ajogun, ya yi kira ga matasa da su yi watsi da rikicin tare da rungumo zaman lafiya.