Rashin Tsaro: Matasa a Jahar Sokoto Sun Fito Zanga-Zanga
Matasa sun fito zanga-zanga a kan titunan garin Goronyo da ke jahar Sokoto.
Sun yi zanga-zangar ne domin neman gwamnati ta kawo musu dauki kan batun rashin tsaro.
Yawan hare-haren ‘yan bindiga yana tilastawa mazauna garin yin hijira zuwa wasu garuruwan.
Sokoto – Wasu matasa a garin Goronyo da ke karamar hukumar Goronyo a jahar Sokoto sun fito kwansu da kwarkwata a tituna suna zanga-zangar halin rashin tsaro da yankinsu ke ciki.
SaharaReporters ta rawaito cewa suna can suna zanga-zangar a lokacin hada wannan rahoton.
Wani majiya ya ce matasan sun fito zanga-zangar ne saboda kallubalen tsaro a yankin, wadda ya tilastawa mutane da dama tserewa daga garin.
Ya ce:
“Ana yin zanga-zanga a garin Goronyo da ke jahar Sokoto. Matasa sun cika tituna suna nuna damuwarsu kan rashin tsaro da ya tilastawa mutane yin hijira barin garin.Suna can suna zanga-zangar a yanzu.”
Hotunan da SaharaReporters ta samu sun nuna an kafa shinge a kan tituna, matasan kuma na kona tayoyi domin nuna rashin jin dadinsu game da kashe-kashe da garkuwa da mutane a yankin.
Sokoto na daya daga cikin jahohin Arewa da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
A baya-bayan nan gwamnatin jahar ta bada umurnin a toshe layukan sadarwa a wasu yankunan jahar don dakile hare-haren ‘yan bindigan.
Toshe layukan sadarwar ya shafi kananan hukumomi kamar Dange Shuni, Tambuwal, Sabon Birni, Raba, Tureta, Goronyo, Tangaza da sauransu.