Babbar Kotu Dake Zamanta a Minna ta Umarci Mohammed Barau Kontagora ya Daina Kiran Kansa Sabon Sarkin Sudan na Kontagora.
Zaben Sabon Sarkin Kontagora ya bar baya da kura.
 Yarimomi 15 sun kai kara kotu kan zargin rashin adalci da magudi.
 Gwamnan jahar ya zabi Mohamma Barau matsayin sabon Sarkin Sudan.
Wata babbar kotu dake zamanta a Minna, birnin jahar Neja a ranar Talata ta umarci Mohammed Barau Kontagora ya daina kiran kansa sabon Sarkin Sudan na Kontagora.
 Wannan umurni ya biyo bayan karar ex-parte da wasu Yarimomi 15 suka shigar kotun.
Wadanda aka kai kara sune Sabon Sarkin , Mohammed Barau Kontagora, Antoni Janar na jahar Neja, Kwamishanan kananan hukumomi da masarautun gargajiya.
 Alkali Abdullahi Mikailu ya umurci Mohammed Barau Kontagora ya daina kiran kansa Sarkin Kontagora “har sai bayan kammala shari’a kan karar da aka shigar ranar 11/10/2021.”
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here