Gwamna Matawalle ya Saka Sabuwar Doka kan Masu Aikata Fashi da Makami

 

Gwamnan jihar Zamfara ya ce ya samu mafita ga matsalar tsaro da ta addabi jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

A daya daga cikin matakan, ya ce za a fara yankewa duk wanda aka kama da laifin bindiganci hukuncin kisa.

Ana yawan samun hare-haren ‘yan bindiga a yankunan Katsina, Zamfara, Niger da dai sauran jihohin makwabta.

Jihar Zamfara – Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu a kan hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin aikata fashi da makami, satar shanu, tsafi, ko kai wa ‘yan bindiga bayanan sirri.

Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a wani sako da ya sanarwa al’ummar jihar a safiyar ranar Talata 16 ga watan Agusta, Punch ta ruwaito.

Matawalle ya ce:

“A ranar 28 ga watan Yuni na wannan shekara, na sanya hannu kan kudirin dokar haramtawa da hukunta masu fashi da makami, satar shanu, tsafi, garkuwa da mutane da sauran laifukan da sukashafe su, 2022.

“Dokar ta ba da wata ka’ida ta doka na hukunta masu aikata laifin fashi da makami.

“Bisa ga sabuwar dokar, duk wanda aka samu da laifin aikata fashi, garkuwa da mutane, satar shanu, tsafi, ko kuma yin aiki a matsayin mai ba da bayanai ga ‘yan bindiga zai fuskanci hukuncin kisa.

“Hakazalika, duk wanda aka samu da laifin tallafawa ta kowacce fuska ga laifukan da aka ambata zai fuskanci hukuncin daurin rai da rai, ko dauri a gidan yari na shekaru 20, ko kuma a dauri a gidan yari na shekaru 10, ba tare da zabin tara ba.”

Dalilin daukar wannan mataki Gwamnan ya bayyana cewa matakan na daga cikin kokarin gwamnatinsa na ganin an shawo kan matsalar ‘yan bindiga da suka addabi jihar da kuma jihohin Arewa maso Yammacin kasar nan sama da shekaru goma.

Ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da gwamnatinsa ta kafu ya fara bullo da dabarun dakile matsalar ‘yan bindiga a fadin jihar.

Ya kara da cewa:

“Abin farin ciki, sabbin matakan sun fara samar da sakamakon da ake so duk kuwa da hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa nan da can.”

Gwamnan ya bayyana ayyukan masu kai bayanai ga ‘yan bindiga a matsayin wani babban sauyi na magance kalubalen rashin tsaro a jihar, inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba lamarin zai zama tarihi.

Ya kara da cewa:

“Game da batun masu kai bayanai, wanda shi ne babban abin da ke kawo cikas wajen yaki da ‘yan bindiga, ina mai farin cikin sanar da jama’ar jihar Zamfara masu son zaman lafiya cewa mun yi nasarar cafke da yawa daga cikinsu.

“A halin yanzu ana yi musu tambayoyi kafin a gurfanar da su a gaban kuliya kamar yadda doka ta tanada.”

A baya dai Matawalle ya bayyana goyon bayansa a baya kan hukunta masu aikata bindiganci, Daily Post ta ruwaito.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here