Tinubu ya Shiga Ganawa da Olusegun Obasanjo

 

Ogun – Ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya dira gidan tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da ke Abeokuta, jihar Ogun.

Daily Trust ta ce, Tinubu tare da rakiyar yan tawagarsa, ya shiga ganawa da Obasanjo a wani ɓangaren cigaba da ziyarar neman shawara da bin matakan cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.

Jirgin Helikwaftan Tinubu ya dira da misalin ƙarfe 1:00 na rana a harabar katafaren gidan Obasanjo (OOPL), Oke Mosan, Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Tsohon gwamnan ya samu tarba daga gwamna Dapo Abiodun na Ogun, mataimakinsa, Noimot Salako-Oyedele, tsoffin gwamnoni, Olusegun Osoba, Gbenga Daniel,da jiga-jigan APC.

Jim.kaɗan bayan isarsa, Bola Tinubu, ya tafi kai tsaye suka fara tattaunawa cikin sirri a gidan Obasanjo da ke harabar Laburari ɗinsa OOPL.

Daga cikin yan tawagar da suka yi wa Tinubu ziyara har da kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, Chief Bisi Akande, Nuhu Ribadu da sauran su.

Ku saurari karin bayani…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here