Matawalle ya Gabatar da Shaidu 19 Gaban Kotu Kan Kalubalantar Nasarar Dauda Lawal

 

Bello Matawalle ya gabatar da shaidu 19 gaban Kotun sauraron karar zaben gwamnan jihar Zamfara.

Bayan sauraron shaidun, Kotun zaɓen ta ɗage zaman ƙarar zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2023.

Ɗaya daga cikin shaidun kuma baturen zaɓen karamar hukumar Maradun ya bayyana yadda aka hana shi faɗin sakamakon da ya tattara.

Zamfara – Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben gwamnan jihar Zamfara ta ɗage zama zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2023, kamar yadda jaridar Tribune online ta ruwaito.

Kotun ta ɗage zaman ne bayan tsohon gwamna, Bello Matawalle, ya gabatar da shaidu 19 domin gamsar da Kotu kan ƙarar da ya kalubalanci nasarar Dauda Lawal.

Matawalle, ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 18 ga watan Maris, ya garzaya Kotun zaɓe ya kalubalanci nasarar gwamna Dauda Lawal na jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan ya ce zaben da aka gudanar cike yake da kura-kurai da maguɗi, bisa haka ya buƙaci Kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara saboda ya samu mafi yawan halastattun kuri’u.

Ya kuma roƙi Kotun ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta hanzarta ba shi sabon satifiket ɗin shaidar cin zaɓe, kamar yadda Punch ta rahoto.

Abinda shaidun suka faɗa wa Kotun zaɓen Zamfara

Yayin ci gaba da sauraron karar ranar Jumu’a, lauyan Matawalle, Usman Sule SAN, ya gabatar da shaidu 19 bisa jagorancin baturen zaben karamar hukumar Maradun, Dakta Ahmad Kainuwa.

Kainuwa ya bayyana wa Kotu takardar sakamakon zaɓen da ya tattara daga kowace gunduma a wani ɓangaren shaidun da Matawalle ya gabatar.

Ya ce kiri-kiri INEC ta hana shi miƙa wannan sakamako kuma ta sanya shi ya sanar da sakamakon zaben da ya tattara daga shafin yanar gizo na INEC.

Ya faɗa wa Kotun cewa sakamakon zaɓen da ya tattara daban da wanda ya gani a shafin hukumar zaɓe.

Amma jami’an hukumar suka umarce shi da ya bayyana wanda yake a Fotal ɗin INEC domin shi ne sahihi.

Bugu da ƙari, Kainuwa ya faɗa wa Kotun cewa an samu tashin hankali a karamar hukumar Maradun kuma DPOn yan sanda ya tilasta masa dakatar da tattara sakamako.

Bayan kammala sauraron shaidun, Alkalin kotun mai shari’a Cordelia Ogadi ta ɗage zaman zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2023.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here