Harin ‘Yan Ta’addan Boko Haram: An Samu Matsalar Kafofin Sadarwa a Yankin Geidam
Mayaƙan Boko Haram sun fara kafa tutocinsu a wasu yankunan ƙaramar hukumar Geidam, kwana biyu da kai harin su garin.
Har yanzun dai mayakan basu bar yankin ba duk kuwa da cewa bataliyar sojojin yankin na nan a yankin, amma hakan baisa sun daina abinda suke ba.
Yan ta’addan sun lalata kayan sadarwa a yankin, wanda hakan yasa ba damar amfani da kamfanonin sadarwa.
Rahotannin dake shigowa yanzun sun nuna cewa mayaƙan Boko Haram sun fara kafa tutar su a wani ɓangare na Geidam, jahar Yobe.
Read Also:
Wannan na zuwa ne bayan kwana biyu da yan ta’addan suka kai hari yankin ƙaramar hukumar Geidam.
Garin na Geidam shine mahaifar muƙaddashin sufetan yan sandan ƙasar nan, Mr. Usman Alƙali Baba.
Wasu daga cikin mazauna garin sun tabbarwa Channels tv cewa yan ta’addan sun kafa tutocinsu a wasu sassan garin.
Hakanan kuma, sun fara yawo gida-gida suna kiran mutane su yarda su amshi aƙidarsu.
Duk da cewa rundunar sojoji dake Geidam ɗin suna nan a yankin, amma hakan baisa yan ta’addan sun daina abinda suke yi ba.
Wasu daga cikin kafofin sadarwar yankin sun sami matsala saboda harin, wanda hakan ya kawo matsalar sadarwa a gaba ɗaya yankin.
Da yawa daga cikim mutanen yankin sun shiga halin ƙaƙa-ni-kayi saboda sun kasa samun damar ji daga yan uwansu saboda matsalar sadarwa a garin.