Gwamnoni da Shugabannin Majalisa za su Gana Kan Matsalolin Tsaro
Gwamnonin Najeriya 36 za su yi ganawar gaggawa domin dinke matsalolin da suka addabi kasar nan.
Hakazalika, a ganawar tasu, shugabannin majalisu daga jihohi za su halarta, duk dai domin nemo mafita ga Najeriya.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke kara fuskantar matsalolin cikin gida, ciki har da tsaro.
FCT, Abuja – Dangane da matsalar tsaro da ake fama da ita a fadin kasar nan, gwamnonin jihohi 36 da shugabannin majalisar dokokin kasar za su yi wani taron gaggawa ranar Juma’a mai zuwa a Abuja, inji rahoton Daily Trust.
Taron dai za a yi shi ne don tattauna matsalolin rashin tsaro da sauran batutuwan da suka shafi kasa baki daya.
Read Also:
Shugaban yada labarai da hulda da jama’a a kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Mista Abdulrazak Bello-Barkindo, ya bayyana a ranar Talata a Abuja cewa mahalarta taron za su yi tunani don nemo hanyoyin magance matsalolin da ke addabar kasar.
Bello-Barkindo ya nakalto Darakta-Janar na NGF, Mista Asishana Okauru, yana cewa:
“Ana sa ran amincewar Majalisar Zartaswa da Majalisar Dokoki za ta mamaye zukatan mutane 72 da za su halarta.”
Daily Sun ta tattaro cewa, ya kuma ambato Okauru na cewa:
“Taron za a yi shi ne don cimma matsaya cikin gaggawa domin kuwa za a gabatar da muhimman batutuwa kamar tsaron rayuka da dukiyoyi a Najeriya baki daya’’.
Sanarwar ta kara da cewa shugaban NGF, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya gargadi gwamnonin da su gaggauta tare da baiwa shugabannin majalisun jihohinsu damar halarta.