Gwamnatin Tarayya ta Saka Mutane 98,000 a Cikin Shirin GEEP 2.0

 

Ma’aikatar kula da harkokin jin ƙai, Agaji da inganta rayuwar al’umma, ta kammala shirye-shiryen ƙaddamar da shirin GEEP 2.0 na kamfanonin gwamnati da shirin tallafi a dukkanin jihohi 36 dama babban birnin tarayya.

Hakan ya biyo bayan tantancewar ƙarshe na masu neman shiga mataki na farko da suka cancanta, kuma aka zabo su don cin gajiyar kananan lamuni na bashi daga N50,000 zuwa N300,000.

Ministar Sadiya Umar Farouq ta ce duk waɗanda suka ci gajiyar shirin na GEEP 2.0 za su rika samun sakonnin taya murna tare da saƙonnin wayar da kai a cikin kwanakin nan masu zuwa domin sanar da su cancantar su tare da jaddada musu cewa shirin na bada rancen kuɗi ne ba tallafi ba.

“Duk waɗanda suka cancanta, nan ba da jimawa ba, za su samu sakon faɗakarwar. Muna so mu tunatar da duk waɗanda suka cancanta, cewa wannan rance ne mai lamuni da ake biya ba tare da kuɗin ruwa ba. Ba tallafi ba ne, Lamuni ne mai sauki wanda dole ne a biya kuɗin da aka karba a cikin watanni 9”.

Minista Sadiya Umar Farouq ta kuma bayyana cewa ma’aikatar na shirin ƙaddamar da shirin a fadin ƙasar, bayan haka kuma za a gudanar da atisayen ƙidayar bayanan waɗanda za su ci gajiyar shirin.

Shirin GEEP 2.0 wani tsari ne na bashi mai lamuni da Gwamnatin Tarayya ta tsara don samar da hada-hadar kudi tare da samar da lamuni ga talakawa da marasa galihu, gami da nakasassu da mutanen da ke fama da rayuwa, waɗanda ke gudanar da kananan ayyukan kasuwancin su a karkashin shirin nata guda uku wanda suka hada da tsarin: (MarketMoni, TraderMoni da FarmerMoni).

Tradermoni yana kai hari ne ga matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 40 yan Najeriya ta hanyar basu rancen kuɗi N50,000 tare da lamuni, yayin da MarketMoni ke kai hari ga mata masu shekaru tsakanin 18 zuwa 55 kamar zawarawa, dama wasu nau’o’in mata masu rauni. Suna samun rancen kuɗi N50,000 tare da lamuni marar riba, da za a biya a cikin watanni shida zuwa tara.

FarmerMoni tsari ne na manoman Najeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 55 a yankunan karkara masu harkan noma. Ana ba su rancen kuɗi tare da lamuni, kimanin N300,000 don bunkasa harkan noma. Wannan tsarin ya kunshi watanni 12 ciki har da lokacin dakatarwa watanni uku 3 da lokacin biya watanni tara 9.

NNEKA IKEM ANIBEZE

SA MEDIA

06-04-2023

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here