PDP ta Mika Sunayen Masu Maye Gurbin Gwamnan Jahar Ebonyi da Mataimakinsa
A yau ne kotu a Abuja ta ba da umarnin a tsige gwamnan jihar Ebonyi bayan da ya koma jam’iyyar APC daga PDP.
Tsigewar ta shafi mataimakinsa, wanda tare da mai gidan nasa suka koma APC; jam’iyya mai mulki a Najeriya.
Jam’iyyar PDP ta tura wa INEC sunayen wadanda take son su maye gurbin gwamna Umahi da mataimakinsa.
Jam’iyyar PDP ta ce ta mika sunayen mutanen da ta amince su maye gurbin gwamnan Ebonyi da mataimakinsa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), TheCable ta ruwaito.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, ta ba da umarnin tsige gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, da mataimakinsa Eric Kelechi Igwe, biyo bayan sauya sheka da suka yi zuwa jam’iyyar APC.
Read Also:
Bayan faruwar lamarin, Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, a wani taron manema labarai a ranar Talata, ya ce jam’iyyar ta zabi Iduma Igariwe da Fred Udogwu a madadin Umahi da Igwe domin ci gaba da mulkar jihar.
Wani bidiyon da PDP ta yada a shafinta na Twitter yana dauke da rubutu kamar haka:
“Bayan tsige Gwamna Dave Umahi da Mataimakinsa Mista Igwe na jihar Ebonyi, kuma bisa ga umarnin kotu, PDP ta mika wa INEC sunayen Iduma Igariwe da Fred Udogwu a matsayin sabon Gwamna da kuma mataimakin gwamnan Jihar Ebonyi”
Jam’iyyar APC a jihar Ebonyi, ta ce babu abin da zai kawo wani dan jam’iyyar PDP kusa da kujerar mulkin gwamnan jihar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Wannan na daya daga cikin lamurran da suke faruwa a APC tun bayan shillawar shugaban kasa Muhammadu Buhari birnin Landon domin duba lafiyarsa.