Rikicin Rasha da Ukraine: Dubban Mazauna Yankin Donbass na Tsere wa Harin
Dubban mazauna yankin Donbass a gabashin Ukraine na tserewa zuwa yammacin ƙasar.
Wakililin BBC Jonathan Beale ya ce sun tarar da wani zungureren cunkoson ababen hawa yayin da tawagarsu ke nausawa cikin yankin – inda ake fafata yaƙin.
A nan ne kuma Rasha ke ƙara ɗaura ɗamarar yaƙi bayan ta janye dakarunta daga arewaci.
Read Also:
Sojojin Ukraine na ba da tsaro a wuraren duba ababen hawa kan dukkan titunan da ke shiga da fita daga yankin.
Kazalika, suna kuma sake tsara hanyoyin kariya tare da wasu ƙwararrun sojan Ukraine a yankin.
Da ma dai sojan Ukraine sun shafe shekara takwas da suka wuce suna yaƙar ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rasha a yankin na Donbas.
Yanzu kuma dakarun Rasha ne ke riƙe da mafi yawan Luhansk da kuma fiye da rabin Donetsk, yayin da suke ƙoƙarin yi wa sojojin Ukraine zobe.