MDD za ta yi Taron Gaggawa Kan Gwaji Sabon Nau’in Makami Mai Linzami da Koriya ta Arewa ta yi
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa bayan da Koriya ta Arewa ta tabbatar da cewa ta gwada wani sabon nau’in makami mai linzami da aka harba a karkashin teku.
Read Also:
Kafafen yada labarai na gwamnati a Pyongyang sun ba da sanarwar cewa sabon makamin ya fadada damar sarrafa makaman Koriya ta Arewa, da kuma sake ba ta wata damar ta kai mamaya har zuwa gaba da yankin tsibirin Koriya a duk lokacin da ta so yin hakan.
Gwajin makamin da aka yi cikin nasara ya saɓa wa umarnin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
Wakiliyar BBC ta ce makamin daya ne daga cikin tarin irinsa da Koriya Ta Arewa ta nuna wa duniya a yayin wani baje kolin tsaro a makon da ya gabata, abin ya haifar da dari darin cewa watakila za ta sake harba wasu.
Amurka ta bukaci Koriya ta Arewa ta guji takalar fada, ta kuma koma teburin sulhu.