Mijina ya Gudu ya Bar ni a Hannun ‘Yan Fashi da Makami – Matar da ta Nemi Kotu ta Raba Aurenta

 

Wata mata mai suna Asiata Oladejo ta fadawa kotu cewa ta rabu da mijinta ne saboda ya gudu ya boye a ban daki ya bar ta a hannun yan fashi da makami.

Abidemi Ya ce matar sa bata da hankali ta kan je shagon sa ba tare da izinin shi ba dan ta da rigima.

Kotun al’ada ta Mapota ta bayar da umarnin hana Asiata Oladejo barazana da yin kutse a cikin rayuwar Abidemi.

Jihar Oyo – Wata mata mai suna Asiata Oladejo, ta shaida wa kotun al’ada ta Mapo a garin Ibadan cewa ta raba aurenta a kan dalilin mijinta, Abidemi ya gudu ya bar ta a hannun ‘yan fashi da makami.

Rahoton VANGUARD Oladejo Asiata ta bayyana hakan ne jiya a kotu yayin da mijinta ya shigar da karar ta.

Oladejo ta fadawa alkali cewa, har yanzu bata gama farfaɗowa daga firgicin da ta shiga a lokacin da gungun ɓarayi suka kai hari gidan su ba.

Ta ce mijinta ko yunkurin kare ta bai yi ba, ya gudu ya boye a bandaki, ya bar ta a hannun ‘yan fashi da makami a lokacin da suka iso gidan da misalin karfe 1 na safe.

“Ni kaina ban san ya boye a bandaki ba. Sai da suka tafi kawai ya fito. Kuma yana tsammanin zan iya ci gaba da zama da shi a wannan gidan,” in ji ta.

Ta ce ta roke shi ya kama musu hayar wani gida, amma ya ki.

Ta zarge shi da kasancewa mai yawan bin matan banza.

Abidemi, wanda ya kasance mai zanen kaya, tun da farko ya ce matarsa ba ta da hankali ta kan zo shagon sa tayi rigima.

Abidmi yace gaskiya ne ya boye a bandaki lokacin da ‘yan fashi da makami suka kai hari gidan su.

Amma duk wani kokari na dawo da ita gida ya ci tura, domin ta ce ta na jin tsoro.

Ya kuma roki kotu da ta ba shi damar kulawar ‘ya’yan su guda uku saboda kasancewar sa uba mai rikon amana.

Akintayo ta baiwa Oladejo kula da yaran uku, inda ta kara da cewa ita ce ta fi dacewa da kula da su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here