Yajin Aiki: Ministan Kwadago ya yi Magana Kan Shirin da Kungiyar ASUU ke yi
Chris Ngige ya yi magana a kan shirin da ASUU ta ke yi na sake yin yajin-aiki.
Ministan yace kungiyar na yawon kiran tafiya yajin-aiki domin tsorata jama’a.
Ngige ya bayyana cewa tun farko ba su karkare magana da kungiyar ASUU ba.
Abuja – Jaridar Punch ta rahoto gwamnatin tarayya tana cewa ba daidai ba ne kungiyar ASUU ta rika zarginta da saba alkawari da yarjejeniyar da aka yi.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana haka a lokacin da ya yi magana da Punch a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, 2021.
Sanata Chris Ngige yace kungiyar ta dogara ne da wani zama da suka yi da Ministan ilmi na kasa, wanda shi Ngige bai ma san yadda zaman na su ya kaya ba.
Kafin magana ta zama yarjejeniya akwai matakan da ake bi. Ministan yace sai maganar ta zo wurinsa, sannan sai ta je gaban majalisar zartarwa ta kasa.
Read Also:
“Da suka ambaci gwamnati, abin ya rikitar da ni, ko suna nufin ma’aikatar ilmi, tattalin arziki, kasafin kudi, ko kuma kwamitin albashi ko ma’aikata ta.
“Idan suka ce gwamnati, suna amfani da harshen-damo ne, suna rikitar da al’umma.”
Ngige yace idan maganar karin albashi ASUU ta ke yi, bayan an gama zama da ma’aikatar ilmi da NUC, za a kai maganar gaban hukumar tsara albashi.
ASUU na barazana da yajin-aiki
Ministan yace ASUU tana yi kamar ba ta san matakan da ake bi kafin a cin ma matsaya ba, kuma ya zarge ta da tado yajin-aiki domin razanar da jama’a.
“Sai suyi ta barazanar za su shiga yajin-aiki, su tada hankalin mutane, wanda hakan bai dace ba.” Dr. Ngige yace an nada sabon shugaban kwamitin da yake tattauna wa da wakilan ASUU, Ministan yace aikin ma’aikatarsa a zaman sa ido ne kawai.
Wani hali ASUU ta ke ciki?
An ji cewa wani jami’in ASUU yace malaman jami’a ba za su shiga yajin aiki a ranar Talata, 31 ga watan Agusta ba, a ranar ne wa’adin da aka bada ya cika.
Dr. Dele Ashiru wanda shi ne shugaban ASUU na reshen jami’ar Legas ya zanta da ‘yan jarida, yace akwai wasu matakan da ake bi kafin a soma yajin-aiki.