Ministan Noma da Raya Karkara ya Auri Budurwa Mai Shekaru 18
Ministan Noma da raya karkara, Sabo Nanono ya yi auri wata budurwa mai shekaru 18 daga Kaduna.
Majiya daga iyalan ministan ta tabbatar da daurin auren inda tuni matar ta tare a gidan ministan a Kano.
Majiyar ta kuma ce iyalan ministan ba su so auren ba duba da banbancin shekaru 50 ke tsakanin ministan da amaryar amma hakan bai hana shi ba Ministan aikin noma da raya karkakara, Sabo Nanono ya auri wata yarinya mai shekaru 18 a wani ɗaurin auren da aka yi cikin sirri kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Mr Nanono, mai shekaru 74 ya auri kyakkyawar yarinyar a auren sirri da mutum uku daga danginsa kadai suka hallarci ɗaurin auren da aka yi a Jere a jahar Kaduna.
Read Also:
“Mutane uku kawai ministan ya wakilta kuma ya gargaɗe su da kada su bayyana wa mutane cewa ya yi aure,” a cewar wani majiya daga iyalin da ya nemi a boye sunansa.
Daily Nigerian ta gano cewa tuni amaryar ta tare a gidan Ministan da ke Tarmandu Close a Kano. Duk da cewa iyalan ministan ba su ya auri yarinyar da ya girma da shekaru 50 ba, majiyoyi sun ce ya tsaya kan bakansa sai da aka yi auren.
“Ministan ya tsunduma kogin soyayya. Bisa dukkan alamu babu abin da zai sauya masa ra’ayi,” a cewar majiyar.
A watan Oktoban 2019, ministan ya ce babu yunwa a Nigeria tunda akwai abinci na N30.
“Abinci na araha a Nigeria idan aka kwatanta da sauran ƙasashe. Misali, a Kano zaka iya cin abincin N30 ka ƙoshi. Don haka mu gode Allah cewar abinci da sauƙi kuma muna iya ciyar da kanmu,” in ji shi.