Corona: ƙasar Burtaniya ta Bada Shawarar Cewa Masu Shekaru Kasa da 30 su Nemi Wani Rigakafin Sabanin Oxford-Astrazeneca

 

Akalla mutum 18 sun rasa rayukansu bayan yin rigakafin cutar Korona.

Bayan watanni ana cece-kuce, an tabbatar da rigakafin na haddasa daskarewar jini.

Yayinda wasu suka samu daskarewa a kwakwalwa, wasu a cikin tumbi suka samu Hukumomi a Turai sun tabbatar da cewa akwai alaka tsakanin daskarewar jini da rigakafin Koronan Oxford-AstraZeneca.

Hakazalika hukumomi a kasar Birtaniya sun bada shawaran cewa matasa yan shekara kasa da 30 kada su yi rigakafin.

A cewar rahoton CNN, hukumar bibiyar magungunan ta Turai European Medicines Agency (EMA) a ranar Laraba ta ce a lissafa daskarewar jini cikin matsalolin rigakafin kuma a rage amfani da shi.

Duk da haka, hukumar EMA ta bayyana cewa amfanin rigakafin ya rinjayi matsalar saboda COVID-19 muguwar cuta ce.

Su kuma hukumomi a kasar Birtaniya sun bada shawarar cewa masu shekaru kasa da 30 su nemi wani rigakafin sabanin Oxford-Astrazeneca.

Za ku tuna cewa irin wannan rigakafin aka kawo wa Najeriya karkashin shirin COVAX. Manyan jami’an gwamnati da jama’a sun yi rigakafin a Najeriya.

Jami’an EMA sun bayyana cewa sun yi bincike kan labarin mutuwar mutum 18. Mutanen na cikin jerin 62 da aka samu da daskarewar jini a kwakwalwa da hanci, yayinda 24 suka samu daskarewa a tumbi bayan musu rigakafin Oxford-Astrazeneca.

A bangare guda, aƙalla 79 sun kamu da cutar daskarewar jini a Burtaniya bayan anyi musu allurar rigakafin Astrazeneca.

Shugaban hukumar ƙayyade magunguna na Burtaniya (MHRA), June Raine, shine ya faɗi haka a wani taro da suka yi.

Shugaban MHRA ya bayyana cewa daga sanda ƙasar ta ƙaddamar da fara yin allurar rigakafin zuwa 31 ga watan Maris ɗin da ya gabata, an yiwa mutane 20 miliyan a karon farko.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here