Ministan Sadarwa ya Jagoranci Bikin Tunawa da Ranar Ƙere-Ƙere ta Duniya

Mai girma ministan sadarwa da tattalin arziƙin fasahar zamani, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), ya jagoranci bikin tunawa da zagayowar ranar nazari da ƙirƙira ta Duniya wanda hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa, CCIE ta shirya.

Bikin na bana wanda aka yi wa take da: Nazari da ƙirƙira na matsayin bunƙasa haɗin gwiwa domin ɗorewar tattalin arziƙin zamani”, an gudanar da shi ne a cibiyar ƙere-ƙeren kayayyakin fasahar zamani ta ƙasa (NCAIR) wacce hukumar ta (NITDA) ta samar a Abuja.

Ranar Nazari da Ƙirƙira ta Duniya rana ce da aka ware domin wayar da kai gami da zaburar da al’umma muhimmancin ƙirƙiro da abubuwa na fasahar zamani waɗanda za su zama mafita kan wata matsala a fannoni daban-daban na rayuwar jama’a daida da tanadin shirin muradi mai ɗorewa na majalisar ɗinkin duniya (UN).

A bikin na bana da ya gudana a wannan rana, mai girma shugaban hukumar ta (NITDA), ya wakilci mai girma ministan na sadarwa wajen miƙa lambobin yabo da kyaututtukan kuɗi ga gwarazan da su ka yi nasarar lashe gasar ƙere-ƙeren inda na ɗaya ya samu kyautar Naira Miliyan Biyu, na biyu ya samu kyautar Naira Miliyan Ɗaya da Dubu Ɗari Biyar, Na Uku Naira Miliyan Ɗaya, sai na Huɗu ya samu kyautar Naira Dubu Ɗari Biyar, kamar yadda aka wallafa a shafin hukumar ta (NITDA) a wannan rana.

Alhamis, 21 ga watan Afrelu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here