Ministan Tsaro Dauke da AK-47: Ma’aikatar Tsaro ta Musanta Jita-Jitar
An yada jita-jitar cewa, an ga ministan tsaro a Najeriya dauke da bindiga AK-47 yayin shiga mota.
Rahotanni da muke samu daga majiyoyi sun bayyana cewa, ba ministan bane, sannan ba ma irin motarsa ba kenan.
Hujjoji sun bayyana cewa, mutumin da ke dauke da bindigar wani shugaban makarantar sojoji ce da ke jahar Benue.
Ma’aikatar tsaro ta musanta ikirarin da ake yadawa cewa mutumin da ke dauke da bindigar AK47 a bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta shi ne minista Bashir Magashi.
Mai taimaka wa Magashi na musamman kan harkokin yada labarai, Mohammad Abdulkadri, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa wanda aka gani a bidiyon shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Muhalli ta Sojojin Najeriya (NACEST) ne da ke Makurdi, jahar Neja.
Read Also:
Ya musanta batun ne a jiya Lahadi 3 ga watan Oktoba, inda ya bayyana cewa lallai ba mai gidansa bane.
Abdulkadri ya yi bayanin cewa duba da yanayin ofis dinsa, shugaban na NACEST yana da ikon doka na daukar makami na doka lokacin tafiya, The Nation ta rawaito.
Mai taimaka wa ministan ya kafa hujja kan ikirarinsa ta hanyar lura da cewa launin kore na Soja a jikin mota kirar Innonson Jeep da kuma alamar NACEST a jikin motar jami’in isassun shaidu ne cewa mutumin ba Magashi bane, Leadership ta kara da cewa.
Ya kara da cewa ministan, kamar takwarorinsa na sauran ma’aikatu, yana amfani da bakar mota ne kirar Land Cruiser jeep.
A kalamansa:
“A zahiri, launin kore na soja a jikin mota Innonson Jeep da sitirar NACEST a jikin motar hukuma cikakkun isassun hujjoji ne na kawar da ikrarin faifan bidiyon da ake magana akan shi a matsayin Babban Ministan Tsaro wanda ke amfani da bakar mota kirar Land Cruiser Jeep kamar takwarorinsa na sauran ma’aikatu.”