Wasu Ministocin Ƙasashen musulmai Sun Shiga Taro

Nijar na karɓar bakuncin taron ministocin harakokin wajen mambobin ƙungiyar ƙasashen musulmi ta OIC karo na 47 a birnin Yamai.

Taron ministocin na ƙasashen musulmi na kwanaki biyu na tattaunawa ne kan taken “hadin guiwa kan yaƙi da ta’addanci, don zaman lafiya da ci gaba.

Tun a ranar Juma’a aka buɗe taron a babban ɗakin taro na Mahatma Gandhi da ke Yamai.

A labarin da ta wallafa game da taron jaridar ActuNiger ta ce, Shugaban ƙasa Mohamadou Issoufou ne ke jagorantar taron tare da sakatare janar na ƙungiyar OIC Dr Yousef A. Al-Othaimeen da kuma wakilan ƙasashe mambobin ƙungiyar 57.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here