Anyi Asarar Rayuka a Rikicin Chadi

 

Mutum aƙalla 22 ne suka mutu sakamakon wani mummunan rikici da ya kaure tsakanin makiyaya Larabawa da manoma da ke zaune a yankin Kabbia da ke kudancin Chadi.

Ana kyautata zaton rashin jituwar ta samo asali ne daga satar shanu da take amfanin gona da ake samu tsakanin al’ummar biyu.

Ministan Sadarwar Chadi, Cherif Mahamat, ya fada wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa ƙauyuka da dama sun ƙone yayin rikicin na ranakun Litinin da Talata.

An kama mutum 66 kuma dokar hana fita ta fara aiki a yankin.

Rikici tsakanin ƙungiyoyin ya kunno kai a yankin Sahel da ke gabar Chadi tun tsawon shekaru da dama da suka gabata.

Chadi na fama da matsalar hare-haren Boko Haram baya ga rikicin Fulani da makiyaya da aka jima ana yi.

Har yanzu sojojin Chadi na ci gaba da yaƙar ‘yan Boko Haram a iyakar ƙasar da Najeriya.

Mahukunta na cewa suna iya bakin ƙoƙarinsu don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here