Shafin da Zai Taimaki Matasa – Sadiya Farouq

Gwamnatin tarayya ta bude sabon shafin da zai taimakawa tsaffin matasan N-Power dman neman tallafi da jari na babban bankin Najeriya CBN, rahoton Leasership.

Wannan shafi da ma’aikatar jinkai da walwala ta shirya tare da hadin kan CBN zai taimakawa wadanda aka cire daga shirin N-Power su shiga domin neman abubuwan alfanu da CBN ke da shi na tallafi, bashi da jari.

A jawabin da Sakataren ma’aikatar, Bashir Nura Alkali ya sake a madadin ministar, Hajiya Sadiya Farouq, ta yi kira ga matasan su shiga shafin domin sanya sunayensu saboda su samu shiga cikin duk wani shiri da CBN ta gabatar.

“An bude shafin NEXIT ne domin ganin inda matasan N-Power zasu samu shiga a shirye-shiryen CBN kuma sai mutum ya cika sharrudan wadannan da CBN ta kindaya,” cewar Minista Sadiya

Ministar ta mika godiyarta ga gwamnan CBN, Godwin Emefiele kan wannan taimako.

Hajiya Sadiya ta yi alkawarin cewa ma’aikatarta za ta cigaba da hada kai da wasu ma’aikatun gwamnati da masu ruwa da tsaki wajen ganin an cimma manufar shugaba Buhari na tsamo mutane milyan 100 daga cikin talauci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here