Kungiyar MOPPAN ta Ja Kunnen ‘Yan Kannywood Kan Tone-Tone da Suke Yiwa Junansu a Shafukan Soshiyal Midiya

 

Kungiyar MOPPAN ta gargadi yan Kannywood da su janye daga yiwa junansu tone-tone a shafukan soshiyal midiya.

MOPPAN ta bukaci yan fim da su zamo masu kishi da kare mutuncin masana’antarsu maimakon kwancewa juna zani a kasuwa.

Tun farko dai rikicin ya kunno kai ne bayan wata hira da sashin Hausa na BBC ta yi da jaruma Ladin Cima.

Kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Najeriya (MOPPAN), ta gargadi yan wasan Kannywood da su daina kwancewa junansu zani a kasuwa musamman a shafukan soshiyal midiya.

Wannan jan kunnen ya biyo bayan rikicin da ya kunno kai a masana’antar cikin yan kwanakin da suka gabata.

A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Al-Amin Ciroma, kungiyar ta ce ta ga akwai bukatar takawa yan wasan birki ne a yayin da ake ci gaba da kace-nace dangane da rigingimun da suka biyo bayan tattaunawar da BBC Hausa ta yi da Hajiya Ladin Cima.

BBC ta nakalto kungiyar MOPPAN tana cewa:

“Mun kula da cewa lamarin ya dauki wani salon a daban. Sannan kuma, zancen na ci gaba da jan hankalin jama’a, musamman mabiya al’amuran fina-finan Hausa, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa dangane da lamarin.

“Hakan ta sa wasu masu ruwa da tsaki suka fara kiraye-kiraye ga shugabannin MOPPAN, da su shiga su magance rigimar.”

MOPPAN ta kara da cewa mutane da kungiyoyi da dama sun aika mata wasiku kan cewa ta dauki mataki a kan lamarin.

Shugaban kungiyar na kasa Dr. Ahmad Muhammad Sarari, ya bayyana cewa duba ga sanin muhimmancin kiraye-kirayen ne ya sa MOPPAN ke tabbatar wa al’umma cewar ta dauki matakan da suka dace kan lamarin.

Ya ce sun yi hakan ne tare da hadin gwiwar sauran kungiyoyi, kamar kungiyar masu shirin fim ta Arewa, wato AFMAN.

Sashin Hausa na BBC ta ce ta sake tuntubar kakakin MOPPAN, inda ya bayyana cewa abun na yan Kannywood yana neman ya wuce gona da iri.

Ciroma ya ce:

“Abu ya faru kan hirar da aka yi da Ladin Cima amma sai jan magana suke ta yi har hakan ta sa an shiga wata gaɓar ta zarge-zarge da jifa juna da kalamai marasa dadi.

“Mafi ban takaici shi ne yadda suka bazama shafukan sada zumunta irinsu Tiktok da Instagram da Facebook, wurare marasa sirri suna harkuza juna.”

Ya kuma ce dole ne MOPPAN ta taka musu burki saboda abin nasu ya koma kai wa juna hari da jifan juna da gore-gore da zarge-zarge da kalaman batanci.

Sannan kungiyar ta bukace yan fim da su kasance masu kishin masana’antar, su kuma daina bin son zuciya da zai iya kawo manyan matsaloli ga sana’ar fim baki daya.

A karshe ta ce za ta duba lamarin dattijai da zaran ta kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here