An Hada Motar da Bata Amfani da Man Fetur a Najeriya

 

Shugaban hukumar zanen motoci a Najeriya (NADDC), Jelani Aliyu, ya bayyana kerarriyar mota mai amfani da lantarki ta farko Najeriya.

Bikin bayyana motar kirar ‘Hyundai Kona’ ya auku ne ranar Juma’a a Abuja kamar da yadda hukumar ta sanar a shafinta na Tuwita.

A cewar sanarwa, za’a yi bikin baja kolin motar na tsawon kwanaki uku daga ranar 5 ga Febrairu zuwa 7 ga Febrairu a wurare daban-daban.

Jawabin yace: “Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola; Dirakta Janar na NITDA, Kashifu Inuwa da sauran manyan baki a bikin bayyana motar Hyundai Kona mai amfani da lantarki da aka hada a Najeriya.”

“Za’a iya bibiyan motocin a wurare irinsu Silverbird Entertainment Center, Banex Plaza, AYA junction Asokoro, Transcorp Junction, Majalisar dokokin tarayyada Federal Secretariat.”

An hada mota maras amfani da man fetur ta farko a Najeriya.

Hukumar cigaban motoci a Najeriya ta bayyana motar kirar Hyundai Kona ranar Juma’a.

A cewar shugaban hukumar, nan ba da dadewa ba Najeriya za ta koma hawa motacin lantarki Gwamnatin tarayyar Najeriya na harin tabbatar da cewa nan da shekaru hudu masu zuwa, kashi 30 na motocin da za’a rika amfani da su a Najeriya su kasance masu amfani da wutan lantarki.

A jawabin da yayi kaddamar da motar lantarki ta farko da aka hada a Najeriya, shugaban hukumar zane da cigaba motoci a Najeriya, Jelani Aliyu, ya bayyana cewa lokacin amfani da mota mai lantarki a Najeriya yayi.

Aliyu ya ce ba za’a bar Najeriya a baya ba yayinda duniya ke cigaba wajen daina amfani da motoci masu amfani da man fetur, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar ta ce kamfanin Stallion wacce ke kan gaba wajen samar da irin wadannan motoci ta zuba hannun jarin $300 million a Najeriya.

Hakazalika, ministan masana’antu, kasuwanci da hannun jari, Otunba Adeniyi Adebayo, ya ce motoci masu amfani da lantarki zasu taimakawa wajen rage amfani da man fetur da kuma lalacewar yanayi Ya ce motar Hyundai Kona da lantarki take amfani dari bisa dari, babu bukatar fetur ko kadan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here