Muhimman Abubuwa Akan Cutar Hawan Jini

Hawan jini cuta ce da ake kamuwa da ita ta dalilin toshewar wasu jijiyoyin jini da suke kai wa ƙwaƙwalwa saƙo, kuma da zarar sun gaza ayyukansu to matsala ta faru.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, cikin wani rahotonta, ta ce akwai kimanin mutum biliyan 1.13 da ke fama da wannan cuta a duniya, kuma kashi biyu cikin uku masu matsakaicin samu ne.

Wani bincike da Hukumar Lafiya ta duniya ta yi a 2015 ya nuna cewa namiji 1 cikin 4 na fama da wannan cuta, yayin da 1 cikin 5 a mata ke fama da hawan jini.

Hawan jini cuta ce mai wahalar sha’ani wadda ba a warkewa daga gare ta da zarar an kamu da ita.

Magungunanta na da tsada – ba irin na su ciwon kai ba ne ko kuma Maleriya.

Idan za a tattara kuɗin maganin da kuka saya a shekara uku saboda wannan cuta za ka ga ba ƙananan kuɗi ba ne.

Cuta ce da kullum ake samun ƙaruwar masu kamuwa da ita wadda kuma take haifar da ciwon zuciya, tana kuma haifar da matsalar ƙwaƙwalwa, ciwon ƙoda da dai sauran cutuka, kamar yadda Hukumar Lafiya ta duniya ta bayyana.

Ƙasa da kashi 1 ne cikin 5 na masu fama da wannan cuta ke iya shan magani yadda ya kamata, shi ya sa da yawa ke mutuwa da wuri kafin lokacinsu ya yi, a cewar hukumomin lafiya.

A Najeriya, wani bincike da aka yi ya ce sama da mutum miliyan 100 ne ke fama da wannan cuta, kuma maimakon raguwa kullum ƙaruwa adadin yake saboda tsarin yadda mutane ke rayuwa, da kuma irin abin da mutane ke ci ko sha, in ji shugaban asibitin koyarwa na Legas Farfesa Adewale Oke.

Saboda rashin zuwa asibiti da yawan mutane na fama da wannan rashin lafiya amma ba ma su san suna da ita ba.

Abubuwan da ke janyo cutar

Ƙiba ko kuma nauyin jiki
Damuwa a kwakwalwa
Shaye-shaye
Yawan cin gishiri
Cutar ciwon siga
Cin abinci mai kitse
Gado
Rashin motsa jiki

Yadda ake lallaɓa cutar hawan jini

Kamar yadda muka bayyana a sama cewa cutar hawan jini na zuwa da wasu cuta masu matuƙar haɗari, amma duk da haka ana iya lallaɓa cutar ta daɗe ba ta tashi ba.

Rage yawan cin gishiri (ƙasa da kilo giram 5 a rana)
Yawan cin ganyaye kayan itace
Motsa jiki akai-akai
ƙauracewa yawan shan taba

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here