Mun Kusa Bude Boda – Ministar Kudi
Bayan shekara daya da hana shigo da kayayyaki ta iyakokin Najeriya, da alamun an kusa budewa.
Farashin kayan abinci musamman shinkafa ya yi tashin gwauron zabo cikin shekara daya.
Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta bayyana cewa da yiwuwan a sake bude iyakokin Najeriya da aka rufe watan Agustan bara, Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana.
Ministar ta laburta a taron tattalin arzikin Najeriya da akayi a Legas cewa kwamitin da shugaba Buhari ya nada don duba ribar rufe iyakokin sun bashi shawaran cewa ya bude, The Sun ta ruwaito.
Read Also:
Saboda haka, tana kyautata zaton cewa Buhari zai dauki shawarar kuma ya aiwatar nan ba da dadewa ba.
Duk da cewa bata bayyana takamammen ranan da za’a bude ba, amma ko shakka babu tace za’a bude nan ba da dadewa ba.
“Mun duba lamuran. Shugaban kasa ya kafa kwamiti kuma dukkan mambobin kwamitin suna masu bada shawaran ya kamata lokacin bude boda yayi.”
“Saboda haka muna sa ran a bude iyakokin nan ba da dadewa ba. Shugaban kasa zai sanar da ranan,” Tace.
Najeriya ta rufe iyakokinta na kasa a Agustan 2019 saboda shigo da makamai, muggan kwayoyi, da kayan masarufi Najeriya daga kasashen dake makwabta.
An rufe iyakokin ne domin karawa manoman shinkafar gida gwiwa domin tabbatar da Najeriya za ta iya ciyar da kanta.