Musabbabin Rikicin ƙasar Sudan

Muna ta jin labarai da dama kan faɗan da ake ci gaba da yi a Sudan a tsawon mako ɗaya da ya gabata, to amma me ya sa ake faɗan?

Rikicin da ya ɓarke a faɗin ƙasar dai ya samo asali ne sakamakon gwagwarmayar iko da mulki tsakanin shugabannin sojojin ƙasar.

Tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Oktoban 2021, Majalisar Janar-Janar ne ke tafiyar da mulkin.

Sojojin biyu da ke wannan takaddama su ne:

Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda shi ne shugaban rundunar sojan kasar kuma a matsayin shugaban ƙasar.
Da mataimakinsa, kuma shugaban dakarun RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti.
Sun samu saɓani kan alkiblar da ƙasar ta dosa, da yunkurin da ake yi na komawa mulkin farar hula.

Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ke ɗaure kai shi ne kan shirin shigar da dakarun RSF mai dakaru 100,000 cikin rundunar soja – da kuma wanda zai jagoranci sabuwar rundunar.

Faɗa tsakanin ɓangarorin biyu ya ɓarke ne bayan kwashe kwanaki ana zaman ɗar-ɗar a yayin da aka sake jibge mambobin dakarun RSF a sassan ƙasar a wani mataki da sojojin ke ganin barazana ce.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here