Elon Musk ya Samu $14bn a Cikin Awanni Takwas

 

Elon Musk ya samu riba sosai da kamfanin Tesla, sai da ya samu $14bn a cikin awanni 8 kwanaki.

Ribar da Attajirin Duniyan ya samu a rana guda, ta zarce gaba daya abin da Aliko Dangote ya tara.

Duk nahiyar Afrika kuwa, har gobe babu mai kudi irin Aliko Dangote wanda shi ne 65 a duk Duniya.

America – Ana maganar Elon Musk wanda shi ne Mai kudin Duniya ya yi asarar Dala biliyan 64.5 a shekarar 2022, amma har yanzu babu mai kudinsa.

Rahoton da Nairametrics ta fitar a kwanakin baya ya nuna cewa a shekarar bana, Attajirin ya yi asarar abin da ya kai Naira tiriliyan 26 a kudin Najeriya.

Duk da haka Musk mai shekara 51 shi ne wanda ya fi kowa kudi a Duniya, har yanzu ba a samu wanda ya ture shi ba domin ya ba Dala biliyan 206 baya.

Mujallar Bloomberg billionaire Index ta ce Aliko Dangote shi ne mai kudin nahiyar Afrika. A jerin Attajiran Duniya, ‘dan kasuwan Najeriyan shi ne na 65.

Elon Musk ya nunka Dangote sau 10 Ko da Dangote ya samu Dala biliyan 1.51 a shekarar nan ta 2022, abin da ya mallaka shi ne $20.6b.

Amma arzikinsa ya yi kasa da kusan -1.7% a watan nan.

A lissafin da ake yi, arzikin Elon Musk mai sama da Dala biliyan 200 ya nunka na Dangote sau goma. Musk ya ba wanda yaki binsa a baya ratar $91b.

Manyan Attajiran Duniya Forbes ta ce a sahun Attajiran Duniya, baya ga Musk sai Bernard Arnoult mai $137b.

Na uku a jerin shi ne Jeff Bezos da $134bn, sai Bill Gates da yake da $122bn.

A wani rahoton da aka fitar, an ji cewa a cikin awanni takwas a Amurka, Musk ya samu abin da ya kai adadin dukiyar da Aliko Dangote ya mallaka a yau.

Tesla ta ci riba a Amurka

Attajirin ya samu wannan makudan biliyoyin daloli ne a yayin da aka bada sanarwar cewa kamfanin motocinsa na Tesla ya tashi da wasu makudan riba.

A ranar 21 ga watan Yunin nan Musk ya samu $14.5bn (Naira Tiriliyan 6.10) a cikin yini guda.

Wannan kudi da ‘dan kasuwan ya samu ya kai adadin dukiyar da Dangote yake tunkaho da ita. A makon da ya wuce, Dangote ya yi asarar kusan N105b ($250m).

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here