Kotu ta yi Watsi da Bukatar Bayar da Belin Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

Babbar kotun tarayya da ke Abuja babban birnin Najeriya ta yi watsi da bukatar bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar ‘yan a-ware ta Biyafara, (IPOB), Nnamdi Kanu.

A lokacin da take yanke hukuncin a yau Talata, Mai shari’a Binta Nyako, ta ce bukatar aba ce da ke zaman cin zarafi ga shari’a, kuma yunkuri ne na ci gaba da magana a kan abin da aka riga aka yanke hukunci a kai.

Sai dai ta shawarci wanda ke neman belin da ya nufi kotun daukaka kara a kan batun, idan bai gamsu da hukuncin ta ba.

Mai shari’ar ta ce tun bayan da aka yanke hukunci a watan Yuli na 2017, lokacin da aka bayar da belin Kanu zuwa yau, an daga shari’ar har sau 15, kuma har yanzu ba a kai ga sauraren ainahin shari’ar tasa ba ma.

Ta kara da cewa ba ta gamsu da dalilan da jagoran na IPOB din yake bayarwa ba na kin bayyana a kotu domin ci gaba da shari’arsa.

Dangane da batun korafin rashin yi masa adalci, Mai Shari’a Nyako ta ce daga bayanan kotun, lauyoyin Kanu na wakiltarsa tun daga ranar da aka soke belinsa, haka ma wadanda suka tsaya masa, kuma ba wani lokaci da aka ki yi masa adalci a shari’ar.

Mai shari’ar ta ce idan har yana son a sake ba shi beli to sai ya yi wa kotu cikakken bayani da zai gamsar da ita kan dalilin da ya sa ya karya ka’idar wancan belin da ta ba shi a baya.

Daga nan sai ta dage sauraren shari’ar zuwa 14 ga watan Nuwamba da kuma jiran sakamakon daukaka karar tasa a kotun daukaka kara.

Kotun ta yanke hukuncin ne na ranar Talata wata daya bayan ta ki bayar da belin jagoran ‘yan a-waren na IPOB a ranar 18 ga watan Mayu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here